Fadar shugaban kasa ta ce kafin a jibge jiragen Tucano da aka samu daga Amurka a yankin Arewa maso Yamma da ‘yan bindiga suka fake, akwai bukatar a bi ka’idojin da aka bi wajen sayen jiragen domin kada Najeriya ta kasance cikin “bakin littafin” kasar Amurka.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ne ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da shirin a gidan talabijin na Trust.
Dangane da abin da gwamnati ke yi na ceto fasinjojin jirgin da aka sace daga Abuja zuwa Kaduna, Shehu ya jaddada cewa sojoji na da bamabamai da za su iya tarwatsa yankin ‘yan ta’addan idan sun ga dama, amma kudurin kubutar da mutane da suka sace a raye yana hana gwamnati baiwa sojoji irin wannan damar.
Ya ce gwamnati ta kuma sanya hannun jari sosai a fasahar jiragen sama mara matuki, yana mai cewa “ana samun nasara sosai da jiragen.”