Gwamnan jihar Anambra, Soludo ya bayyana cewa gwamnatinsa ta kori malamai kusan 1,000 saboda basu cancanci koyar da dalibai ba.
Gwamnan ya kara da cewa gabadaya malaman daya kora duk ba ingantattu bane kuma bai kori ingantaccen malami ko daya ba.
Soludo ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a wata wasikar da sakatarensa Mr Chris Aburime ya rattabawa hannu.