fbpx
Thursday, August 18
Shadow

“Dalilin dayasa ake cigaba da fuskantar matsalar tsaro a Najeriya”:>>Atiku Abubakar

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana dalilin dayasa ake cigaba da samun matsalar tsaro a Najeriya.

Ya bayyana hakan ne biyo bayan harin da ‘yan Boko Haram suka kaiwa babban gidan yari na Kuje dake Abuja.

Inda yace dalilin dayasa ake cigaba da fuskantar matsalar tsaro shine gwamnati bata kama masu aikata laifin tana hukunta su sai yasa suke cigaba da abinda sukaga dama.

Kuma Atiku ya bayyana bacin ransa akan harin da aka kaiwa gidan yari na Kuje dake babban birnin tarayya Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published.