Kungiyar Inyamuran Najeriya ta Ohanaeze Ndigbo ta bayyana dalilin dayasa har yanzu bata kaddamar da wani dan takarar shugaban kasa ba.
A baya dai kungiyar ta nemi jam’iyyun Najeriya cewa su baiwa ‘yan kudu masu gabashin Najeriya tikitin shugaban kasa.
Kuma ita kungiyar yarabawa ta Anifere ta kaddamar da Peter Obi a matsayin dan takararta, inda tace Inyamurai ya kamata a baiwa mulkin kasar idan har anaso ayi adalci.
Amma ita kungiyarsu ta Ohanaeze tace bata kaddamar da wani dan takarar bane domin al’ummarta sun rigada sun san wanda yafi cancanta a wurinsu, kuma shi zasu zaba.