Hukumar zabe ta INEC ta bayyana sunayen ‘yan takarar sanata da suka lashe zaben fidda gwani kuma wa’yanda jam’iyyu suka bayyana mata.
Amma sai dai duk da cewa APC ta bayar da sunayen shugaban sanatoci Ahmad Lawal, Godwill Akpabio da gwamna David Umahi INEC taki saka sunayen su a cikin jadawalinta.
Inda babban kwamishinan hukunar zaben Fetus Okoye ya bayyana dalilin dayasa hakan ya faru, yace sunki saka sunayen nasu ne saboda akwai lauje cikin nadi dangane da ‘yan takarar guda uku.
Inda yace babu tabbacin cewa sunyi zaben fidda gwani na sanata, domin sun nemi takarar shugaban kasa sun fadi kuma a watan mayu akayi zaben fidda gwani na sanatocin APC na shugaban kasa kuma a watan yuni.
Amma duk da haka dai jam’iyyar APC tace gabadayansu sunyi zaben fidda gwanin, Lawal na neman sanatan arewacin Yobe ne, Godwill kuma arewa maso yammacin Delta sai umahi kudancin Ebonyi.