Shugaban karamar hukumar Wase dake jihar Plateau, Ado Buba ya bayyana cewa suna cigaba da siyawa ‘yan vigilanti bindugu saboda matsalar tsaro tayi yawa a yankin.
Inda yace izuwa yanzu sun saya masu manyan bindugu guda 80 kuma sun raba masu saboda su taimaka wurin kare rayukan al’ummar yankin.
Ado Buba ya bayyana hakan ne yayin dayake ganawa da kwamitin majalissar wakilai ranar alhamis.
Inda kwamitin ke bincike kan kananun hukumomin da suke fuskantar matsalar tsaro a jihar.