Tsohon shugaban sanatoci, Bukola Saraki wanda ya fadi zaben fidda gwani na shugaban kasa a jam’iyyar PDP ya bayyana dalilin dayasa ya hana Tinubu tsayawa a matsayin mataimakin shugaba Buhari a shekarar 2015.
Tinubu ya bayyana cewa Saraki ne da wasu mutane suka hana shi tsayawa a matsayin mataimakin shugaba Buhari saboda shi Musulmi ne.
Inda Saraki ya bayyana cewa ko gobe za a sake yin zabe ba zai bar Musulmi da Musulmi suyi mulki ba sadoda baya son a hada fada da kirista.