fbpx
Saturday, August 13
Shadow

Dalilin dayasa na yiwa Tinubu lakabi da Jagaban, Sarkin Borgu

Dakta Halliru Dantoro sarkin Borgu ya bayyana dalilin dayasa ya lakantawa dan takarar shuganan kasa na APC, Bola Ahmad Tinubu sunan Jagaban.

Inda yace yayi hakan ne don girmama shi bisa amarsa da kuma taimaka masa da yayi a lokacin da suke sanatoci,

Domin Tinubu na taimaka masa sosai kuma yana bashi shawara akan al’amuransa duk da cewa ba jam’iyyar su daya, a lokacin Tinubu na jam’iyyar SDP shima yana NRC.

Saboda haka ne daya samu sarautar Borgu yace ya kamata ya yiwa Tinubu sakayya, sai yasa ya bashi sunan Jagaban watau shugaban jarumai.

Leave a Reply

Your email address will not be published.