fbpx
Saturday, June 10
Shadow

“Dalilin dayasa shugaban Buhari ya fifita Osinbajo akan sauran masu neman shugabncin Najeriya”>>El Rufa’i

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El Rufa’i ya bayyana cewa farfesa Yemi Osinbajo ne zabin shugaba Buhari a cikin yan takarar dake neman shugabancin Najeriya.

Gwamnan ya bayyaba hakan ne jiya yayin da Osinbajo ya kai ziyara jihad Kaduna domin ganawa da wakilan APC gami da zaben fidda gwani mai zuwa.

Inda yace shugaban kasa da gwamnoni da mutanen Najeriya bakidaya suna girmama farfesa Yemi Osinbajo, kuma yana son jihar Kaduna sosai.

A karshe yace ba neman zabe ne kadai ya kawo Osinbajo jihar Kaduna ba, yazo ne don ya nunawa mutanen garin irin kaunar dayake masu.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *