fbpx
Friday, January 15
Shadow

Dama can kana da gadon Hauka>>Sanata Shehu Sani ya gayawa Dan Gwamnan Kaduna, Bashir El-Rufai

An yi wata ‘yar Dirama tsakanin Sanata Shehu Sani, tsohon me wakiltar Mazabar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattijai da kuma dan gwamnan Kaduna, Bashir El-Rufai.

 

Lamarin ya farune a shafin Twitter inda Sanata Shehu Sani ya fara saka hoto yana nuna yanda masu mulki suke kamin zabe da kuma bayan sun ci zabe.

Dan gidan Gwamnan Kadunan, watau Bashir shima sai ya saka hoton Sanata Shehu Sani inda yake tare da Buhari da kuma wani hoto inda yake shi kadai, da alamun damuwa a tare dashi.

 

Yawa hoton taken Kamin Murus da bayan Murus.

Saidai ga dukkan alamu abin baiwa Sanata Shehu Sani dadi ba inda ya mayar masa da martanin cewa,ka yi gadon gajarta da hauka.

Saidai bashir ya bashi amsar cewa,Allah Sarki.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *