Biyo bayan rushe kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC da tsohon shugaban ta, Adams Oshiomhole ke jagoranta, da jam’iyyar ta yi bisa shawarar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da dama sun yi amannar cewa dangantaka ta yi tsami kenan tsakanin shugaban kasan da Bola Ahmad Tinubu, wanda mutumin Oshiomhole ne.
Saidai fadar shugaban kasar ta fito tace babu wata tsamin dangantaka tsakanin shuwagabannin 2. Amma duk da haka, jigo a kungiyar kare muradun Yarbawa ta, Afenifere, Ayo Adebanjo yace Shi dama yasan tun tuni Shugaba Buhari yaudarar Tinubu yayi kawai dan ya samu abinda yake so.
Yace Shima Tinubun Yaudarar shugaban kasar yake ba dan ci gaba aka kafa jam’iyyar ba an kafatane dan rabon mukamai da cimma buruka. Yace sun dade a siyasa sun san duk wani salonta.
Yace amma abinda ya kamata Tinubu da Osinbajo su yi shine su maida hankali wajan ganin an canjawa kasar Fasali, hakanne kawai zai amfani al’umma musamman yankin Yarbawan.