fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Dama Dan Can Dan Kwaya ne>>Dailytrust tawa Fani Kayode zagin kare dangi

Bayan cin zarafin da yawa wakilin jaridar Daily Trust, Eyo Charles a jihar Cross-Rivers, Tsohon Ministan Sufuri, Femi Fani Kayode da alama ya debo da zafi. A baya yace ba zai taba bada hakuri ba amma da Allah wadai ta yi yawa akan abin da yawa dan jaridar ya fito ya bada hakuri in yace yasan yayi abin kunya.

 

Saidai ga dukkan alamu JAridar ta Daily Trust bata yafe abin da yayi ba, A wata Wallafa da ta yi me matukar daukar hankali,Daily Trust ta bayyana FFK a matsayin dan kwaya, tace da yaje kasashen Turai karatu ya yi ta taammuli da miyagun gwayoyi ta yanda har abin ya zamar masa jiki.

 

Tace saida yayi ta neman magani hadda na gargajiya, kai harkasar Ghana ya je amma ga dukkan alamu har yanzu be warke ba. Ta ce ko da a jam’iyyarsa ta PDP babu me daukarsa da muhimmanci saboda yanda yake zubarwa da kansa girma, hakanan a mazabarsa ma basu yadda su zabeshi ya wakilce su ba kuma har abada da wuya hakan ta faru.

Karanta wannan  Nasan ku jajirtattu ne ku riga kora 'yan bindiga idan sun kawo maku farmaki, Gwamnan jihar Ondo ya fadaw 'yan jiharsa

 

Daily Trust tace tabin Kayode ne ya motsa a lokacin da yawa wakilinsu cakwaikwaiwa kuma ya nunawa Duniya ko shi wanene.

 

Wannan Rubutu dai da Daily Trust ta yi ya dauki hankula sosai inda wasu ke ganin tunda ya bada hakuri da ta kyaleshi, wasu kuma na ganin cewa hakan da ta yi yayi daidai dan kuwa shima haka yake gayawa mutane abinda yaga dama.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.