Tsohon dan majalissa, Shehu Sani yayi tsokaci akan maganar da Bola Ahmad Tinubu yayi ranar biyu ga watan yuni, cewa shine ya tsayawa shugaba Buhari ya zama shugaban kasa a shekarar 2015.
Inda Shehu Sani yace tabbas Tinubu ya taka muhimmiyar rawa a nasarar da shugaba Buhari yayi na zaben shekarar 2015, amma sai ita siyasa dama haka ta gada ba amana.
Tinubu ya bayyana cewa har Katsina yaje ya samu Buhari cewa ya fito zai mara masa baya kuma yayi nasara, amma bai bashi minista ko kuma wata kwantiraki ba.
Sannan kuma gashi yanzu gashi da yiyuwar ba zasu tsayar da shi a matsayin dan takarar APC ba, amma dai ranar 6 ga watan yuni zasu gudanar da zaben na fidda gwani.