fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Dambarwa: Abba Kabir Yusuf ya shigar da Ganduje kara bisa zargin karkatar da Otal din Daula ga wani Dankasuwa a jihar Kano

Da’alamu siyasar Kano ta fara daukan wani sabon salo, wanda a ‘yan kwanakin nan anjiyo ita kanta kungiyar kwankwasiyya ta kai karar gwamnatin jihar Kano bisa kudirinta na samar da jirgin kasa a cikin birnin jihar wanda gwamnatin jihar ta shirya ciyo bashin sa.

Shima dan Takarar jam’iyyar PDP a shekarar 2019 Abba Kabir Yusuf ya shigar da gwmanatin jihar kano kara, inda yake zargin cewa gwamnatin ta ware wasu gine-gine mallakar jihar ga wasu ‘yan kasuwa a jihar.

Gine-ginan dai sun hada da Otel din Daula wanda gwamnatin ta mallakawa wani Dankasuwa Da ya shahara A jihar Muddansir Idris, haka zalika gwamnatin ta mallakawa wani Dankasuwa wajan ajiye motoci na Shahuci ga wani Dankasuwa Al-Samad.

Karanta wannan  ZABEN 2023: Idan Muka Yi Sake Atiku Zai Iya Cin Banza, Cewar Kwankwaso

Dan takarar gwamnan na Jam’iyyar PDP ya bayar da hujjar cewa matakin da gwamnatin jihar Kano ta dauka na baiwa kadarorin ga Mudatex da El-samad wadanda suke masu zaman kansu sun sabawa sashe na 1, na dokar amfani da kasa,, da sashe na 44 (1) na kundin tsarin mulkin 1999 da a kaiwa gyra.

Sauran wadanda ake kara sun hada da Mudassir Idris, El-Samad Nigeria Ltd, Ofishin kula da filaye na jihar Kano, Ma’aikatar Ayyuka da inganta ababen more rayuwa, Ma’aikatar Gidaje da sufuri, haka kuma Babban Al’kalin jihar Kano.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.