Monday, October 14
Shadow

DAMBARWAR MASARAUTAR KANO: Lauyoyin Sarki Aminu Ado Bayero Sun Janye Daga Tsaya Masa

DAMBARWAR MASARAUTAR KANO: Lauyoyin Sarki Aminu Ado Bayero Sun Janye Daga Tsaya Masa

Daga Bashir Gasau

Babbar Kotun Jihar Kano me Lamba 7 dake zamanta a sakatariyar Audu Baƙo, ƙarƙashin jagorancin me shari’a Amina Adamu Aliyu, ta ce tana da hurumin sauraron ƙarar da Gwamnatin Kano da sauran wasu ɓangarori suka shigar.

Alkaliyar ta bayyana hakan ne a lokacin da take yin ƙwarya-ƙwaryar hukunci akan batun hurumin kotun, a yayin zaman kotun na yau Alhamis harma ta ayyana ranar 15 ga watan nan da muke ciki a matsayin ranar da za ta ci-gaba da sauraron Shari’ar.

Toh sai dai bayan ƙwarya-ƙwaryar hukuncin kotun, Lauyoyin Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero suka fice daga kotun harma kuma bayyana cewa, zasu je su zauna da sarkin domin neman sabbin lauyoyin da zasu ci-gaba da tsaya masa a Shari’ar.

Karanta Wannan  'Ya kamata a ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro a Najeriya'

Babban Lauyan Jihar Kano da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar dama Majalisar Dokokin jihar ne suka shigar da ƙarar, inda suka nemi kotun ta hana Aminu Ado Bayero da sarakunan Bichi da Rano da Gaya da kuma Ƙaraye ci-gaba da ayyana kansu a matsayin Sarakuna.

Kuma dai waɗanda sukai ƙara sun haɗar da Sarakunan da gwamnatin kano ta soke guda Biyar, Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Daraktan Hukumar tsaron farin kaya DSS, Jami’an Tsaron Civic defense da rundunar Sojojin Najeriya.

MAJIYA: GTR Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *