Kamar yadda wani sashin waƙar ke cewa, “Ni ce mai rinjaye, kuma dole zan mulke ka, ka kuma bi umarni na matuƙar muna tare.”
Amarya ta tashi ta dinga rawa tare da girgijewa, lamarin da ya fusata Ango da danginsa har ta kai ga an yi kaca-kace da ƴan uwan amarya.