Babban dansandan Najeriya da aka kama bisa laifukan safarar gwaya da kuma damfara, watau DCP Abba Kyari ya roki kotu da kada a kaishi kasar Amurka.
Abba Kyari yayi rokon ne inda yake cewa kamun da aka mai na da alaka da siyasa.
Kyari yace kawai ana son a daina yaki da masu laifi ne shiyasa aka kamashi.
Kyari yace laifukan da ake zarginsa akai basu kai a kamashi a kaiwa kasar Amurka ba, yace tsabar nuna kiyayya ne.
Hakanan kuma Kyari ya bayyana cewa, Hushpuppi da ake alakantashi dashi, yana ma bincike akansa ne yayin da aka kamashi.