fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Dan fashi ya dirkawa abokin fashinshi harsashi

Wani dan fashi daga jihar Ondo ya bindige abokin fashinshi yayin da suke kan hanyar tserewa bayan kwacewa wata mata dake shagon OPS Dubu 60.

 

Lamarin ya farune a yankin Okitipupa inda bayan sun yi fashin suna neman tserewa sai matar da suka sacewa kudin ta kurma Ihu. Jama’a sun rufarwa ‘yan fashin, da daya daga ciki yaga ana neman kamasu sai yayi harbi a iska, garin hakane ya bindige abokin aikin nasa.

‘Yansanda sun dira wajan da lamarin ya faru inda suka dauke gawar Wanda ya mutu da aka bayyana sunanshi da Kehinde inda suka samu kudin da aka yi fashin da kuma bindiga.

Karanta wannan  Dirama: Yara 23 da aka ceto a hannun fasto sunki amincewa su koma ga iyayensu

 

Sun tabbatar da cewa nan ba da dadewa ba za’a kamo wanda suka tsere.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.