fbpx
Friday, July 1
Shadow

Dan Gidan Ango Abdullahi Ya Lashe Zaben Fidda Gwani Duk Da Yana Tsare A Hannun Masu Garkuwa Da Mutane

Daga Abubakar A Adam Babankyauta

Sadik Ango Abdullahi ya samu tikitin tsayawa takarar dan Majalisar dokokin jihar kaduna a daidai lokacin da masu Garkuwa da mutane ke rike da shi.

Sadik Ango Abdullahi ya samu galaba a kan ‘yan takarar majalisar wakilan tarayya a Sabon Gari Idan abubuwa sun tafi daidai, Ango Abdullahi ne zai yi wa PDP takarar ‘dan majalisa a zaben 2023

Har zuwa yanzu babu tabbacin Sadik Ango Abdullahi ya bar hannun masu garkuwa da mutane.

Sadik Ango Abdullahi ne wanda ya samu nasara a zaben tsaida gwani da jam’iyyar PDP ta shirya a karamar hukumar Sabon Gari, jihar Kaduna.

A ranar 23 ga watan Mayu 2022, jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa Sadiq Ango Abdullahi ya tika sauran masu neman takara a jam’iyyar PDP.

Rahoton ya ce a zaben fitar da gwanin da aka gudanar jiya, Ango ne ya zo na farko, ya doke sauran abokan hamayyarsa duk da bai dade da shiga jam’iyyar ba.

Karanta wannan  Ɓarayi Sun Harbi Mutum Daya Tare Da Ƙwace Ƙudaɗen Hannunsa A Jihar Katsina

Ango Abdullahi ya samu kuri’a 28, yayin da Hajiya Hadiza Muhammad. Salisu Abdulhamid da Misis Pauline ne suka zo na biyu, uku da na hudu a zaben.

Hakan ya na nufin Sadiq Ango Abdullahi shi ne wanda zai yi wa jam’iyyar PDP takara a mazabarsa ta Sabon Gari da ke garin Zaria a zabe mai zuwa.

Ayanzu haka Sadik Ango Abdullahi na hannun miyagun mutane masu garkuwa da mutane.

Sai dai har zuwa yanzu Sadiq Ango Abdullahi yana cikin mutum 61 da aka yi garkuwa da su a jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja tun a karshen watan Maris.

Har zuwa yanzu da mu ka samu rahoton nan, babu tabbacin ‘dan siyasar ya kubuta. Kwanaki aka yi ta rade-radin cewa ya fito, amma babu wanda ya gan shi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.