Dan gidan Tsohon gwamnan Kano, Umar Abdullahi Ganduje ya yi rashin nasara a karar da ya shigar yana kalubalantar zaben Abdulkadir Jobe a matsayin dan majalisa me wakiltar Rimin Gado, Dawakin Tofa, Tofa, a majalisar tarayya.
Kotun sauraren kararraki a Kano ranar Talata ta yi watsi da karar da dan gidan Gandujen ya shigar.
Umar yayi zargin cewa, an gudanar da zabenne ba bisa doka ba inda aka tafka magudi.
Kotun dai tace karar bata da isashshiyar hijja.