Dan gidan gwamnan Kaduna,Bello El-Rufai ya bayar da hakuri kan cece-kucen da ya hadashi da wani a shafin Twitter har ya mai barazanar lalata da mahaifiyarshi.
Lamarin ya jawo cece-kuce sosai inda har mahaifiyar ta Bello, Hajiya Hadiza ta shiga ciki.
A yanzu dai Bello yace ba haka aka mai tarbiyya ba kuma yana baiwa kabilar da ya caccaka saboda laifin mutum 1 hakuri, yace shima mutumin yana bashi hakuri.
Ya kara da cewa ya kuma baiwa mahaifiyarshi hakuri.
My apology. pic.twitter.com/t3JKHeJNY0
— Bello El-Rufai (@B_ELRUFAI) April 17, 2020
Wasu dai sun yaba da wannan hakuri da Bello ya bayar yayin da wasu suka ki karba.