fbpx
Wednesday, May 25
Shadow

Dan gidan tsohon shugaban kasar Libya Saif Al-Islam Ghaddafi zai tsaya takarar shugabancin kasar a shekara me zuwa

Gaddafi's son Saif al-Islam to run for Libya president in 2018
Dan gidan tsohon shugaban kasar Libya, Saif Al-islam Ghaddafi zai tsaya takarar shugabancin kasar Libyan a shekarar 2018 me zuwa, kamar yanda wata majiya daga iyalanshi suka bayyanawa kafar watsa labarai ta Egypt Today, haka kuma majiyar ta bayyana cewa Saif Al-Islam yana da goyon bayan mafi yawa daga cikin kabilun kasar ta Libya.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Kasar Libya dai ta daidaice yanda kunsan ‘yan tawayene daban-daban rike da makamai suke mulkin bangarori daban-daban na kasar, amma ana saran wata hadakar kungiya dake mulkin da majalisar dinkin Duniya ta amince da shi a kasar da ake cewa GNA, a takaice, zata shirya zabe a shekara me zuwa.

Karanta wannan  'Yan IPOB sunce sojoji su fice daga jihohin Inyamurai
Kuma Saif yayi alkawarin kawo karshen tashin tashinar da ake samu a kasar.
Shidai Saif AL-Islam wata kotu a kasar ta yankemai hukuncin kisa kuma wasu ‘yan tawaye sun kamashi suka tsareshi na shekaru shida amma a wannan shekarar cikin watan Yuni aka sakoshi.
Amma kotun Duniya ta ICC ta bukaci a kamashi bisa zargin laifukan cin zarafin bil’adama a lokacin mahaifinshi na kokarin dakile ‘yan tawaye da suka taso.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.