fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Dan kudu APC zata tsayar takara a shekarar 2023>>Wani na hannun damar Buhari ya tabbatar

Wani tsohon soja wanda yayi yakin basasa sannan kuma abokin shugaba Buhari ne na tsawon kusan shekaru 50 ya bayyana cewa jam’iyyar APC a shekarar 2023 dan kudu zata tsayar takarar shugaba  kasa.

 

Kyaftin Joseph Din me murabus wanda kuna jigo ne a jam’iyyar APC ya bayyana cewa, idan shugaba Buhari ya kammala mulki dan kudu za’a baiwa.

Saidai dan kudun ba’a san daga wane bangare zai fito ba. Ya bayyana cewa shugaban kasar, Abokinsa yayi matukar kokari musamman wajan dakile kungiyar Boko idan aka kwatanta da shekarar 2015.

Karanta wannan  APC ta gaza domin shugaba Buhari bai damu da ilimin Najeriya ba, cewar daliban Najeriya

 

Yace shugaba Buhari mutumin kirkine wanda ba’a hada kai dashi a yi abinda bai kamata ba. A hirarsa da Sunnews ya kara da cewa Najeeiya ta yi sa’a da ta sameshi a matsayin shugaba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.