fbpx
Monday, August 8
Shadow

Dan majalisar jihar Filato, matarsa, yaransa sun tsallake rijiya da baya yayin da wasu ‘yan bindiga suka kai wa ayarin motocinsa hari

Dan majalisar a hagu, Shugaban jami'iyyar PDP a dama

Dan majalisar a gefen hagu, Shugaban jami’iyyar PDP a gefen dama

Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan ta’adda ne a daren ranar Talata, 19 ga watan Afrilu, sun yi wa ayarin sabon zababben dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Jos ta Arewa/Bassa a majalisar wakilai, Musa Agah Avia kwanton bauna.

Dan majalisar tarayya tare da matarsa ​​da ’ya’yansa da kuma mukarrabansa an ce suna dawowa gida ne daga rangadin godiya da misalin karfe 9 na dare a lokacin da lamarin ya faru a kan Twin Hill Miango, a karamar hukumar Bassa ta jihar.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, mataimaki na musamman ga dan majalisar, Moses Maly, wanda ke cikin mota daya tare da shi, ya ce wasu mutane biyu da ke kan babur a gaban ayarin motocin sun fara cin karo da ‘yan bindigar ne kuma aka kashe su a harin kwantan bauna.

Karanta wannan  A rika sanar dani daga yau domin ba zan laminci kashe mutane a kudu maso gabashin Najeriy ba, cewar shugaba Buhari

Sai dai Dan majalisar, matarsa da kuma yaransa sun tsallake rijiya da baya.

Wadanda aka kashe sun hada da shugaban jam’iyyar PDP ward Kimakpa, Hon. Timothy Weyi da shugabar mata.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.