Asalin dan Najeriya da Izuchukwu da hukumar kasar Indiya ta kama da kwaya ta kaishi gidan Kurkuku ya mutu a cewar hukumar.
Matashin dan shekara 38 ya mutu ne ranar litinin sakamakon kamuwa da ciwon bugun jini wanda yayi sanadiyar rayuwarsa a cewar rahotanni daga kasar Indiya.
Kuma hukumar ‘yan sandan ta bayyana cewa sun kai shi asibiti wanda a can ne wa’adinsa ya cika.
Hukumar ta kama shi a ranar 14 ga watan Yuli kuma ta maka shi a kotu da kaifin safarar miyagun kwayoyi yayin da kotun ta daga karan izuwa 29 ga watan Yulin amma yanzu ya mutu.