fbpx
Saturday, June 25
Shadow

Dan Nijeriya Kuma Babban Malami A Addinin Musulunci Ya Fito Da Sakamakon Mafi Daraja A Matakin Daktarin Kasar Sudan

Dan Nijeriya Kuma Babban Malami A Addinin Musulunci Ya Fito Da Sakamakon Mafi Daraja A Matakin Daktarin Kasar Sudan

Daga Comrd Yusha’u Garba Shanga

Shahararren Malamin Addinin Musulunci wanda yake zaune a kasar Sudan Sheikh Muhammad Abubakar Yawuri, wanda aka sani da Mallam Saminaka, ya gama karatun Dakta akan Nazarin Addinin Musulunci da kuma Yaren Larabci.

Malamin Yasamu Digirinsa na ukune daga Jami’ar Salam dake babban Birnin Khartoum na Kasar Sudan.

Malam Saminaka dai ya kasance Malami ne da kusan duk Daliban Najeriya dake Sudan sun anfana da Iliminsa, tare da fa’idantuwa da sukayi dashi cikin fannonin ilimin addinin Islama.

Karanta wannan  'Yan ta'addan siyasa sun tayar da hankulan al'umma sun hana su yin rigistar katin zabe a jihar Osun

Malamin Dan asalin jihar Kebbi ya Shahara a fagen da’awa a kasashen Sudan da Najeriya, yayinda ya zamo bijimi a fannin Yaren Larabci, Fiqhu, Hadith da kuma sauran Fannonin na Ilimi.

Malam Saminaka shine Malamin dayake gabatar da Shirin Zauren Fiqhu a wannan tasha ta New Africa Hausa.

Tashar Africa New tare da sauran Al’ummar Musulmi na taya Malam Saminaka Murnan Kammala Karatunsa na Dakta da Sakamako mafi girma wato First Class, dafatan Allah ya Albarkaci karatunsa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.