Wani jami’in dan santa mai suna Zeus yaci mutunci wani mutun Okoye tare da matarsa mara lafiya ranar litinin da dare misalin 9 zuwa 1.
Okoye yana hanyar dawowa daga asibiti ne tare da matar sa mara lafiya sai dan sandan ya tare shi ya duba motarsa kuma yace masa ya bashi cin hanci.
Sai Okoye yace masa daga asibiti yake ko sisi babu a hannun shi ya kashewa matarsa mara lafiya kudin, wabda hakan yasa ya fusata ya kwace masa takaddun mota kuma ya lakada masa duka.
Okoya ya kira wani abokinsa dan sanda yaba Zeus wayar sukayi magana, amma duk da haka bai sake su ba har sai abokin nasa yazo ofishin da misalin karfe 1 da rabi na dare karin ya barsu suka tafi gida.