fbpx
Thursday, July 2
Shadow

Dan Sarki Sanusi II da aka Tsige ya mayar da martani kan lamarin

Da a Gurin Sarkin Kano,Muhammad Sanusi II da gwamnatin Kano ta tsige ranar Litinin, watau Adam Lamido Sanusi ya mayar da martani akan sauke mahaifin nasa daga kan karagar Mulki.

 

A wani Rubutu da yayi a shafinsa na sada zumuntar Instagram, Adam ya bayyana godiyarsa ga ‘yan uwa da abokan arziki da suka kira suka jajanta masa kan wannan lamari.

 

Ya kara da cewa, kamar yanda yake a koda yaushe, kowane bangare na da dalilinsu na yin abinda suka yi. Yace a matsayinshi na da a gurin Sarki Sanusi dole abin akwai ciwo kuma yana goyon bayan mahaifin nasa. Yayi kira da cewa kada a zagi Wani da sunan Mahaifinsa dan kauwa shima ba zai so a zagi mahaifinsa ba.

 

Yace mahaifin nasa ya gaya mai cewa, Idan yana so ya kawo canji,kada ya rika kallon wane matsayine ya kamata ya samu dan ya kawo canjin,maimakon haka yayi kokarin kawo canjin a cikin matsayin da yake, ta hakane har zai kai kan matsayin da zai kawo canjin daya kamata. Yace dan haka wannan lamari dariya yake bashi dan yasan cewa mahaifinsa zai wareware dagashi.

 

Adam ya yiwa jama’ar Kano Fatan Alheri inda yace zai yi kokarin fafutuka dan kawo ci gaba ko yana da mukami ko bashi da shi.

 

View this post on Instagram

Thank you all so much for your messages and well wishes. As is with all cases each side has their reason for why they do things. As a son it should be painfully obvious who has my support but I do not want my father to be insulted more than I want to make comments myself so keep my peace and I also ask that you not insult others on his behalf. MSII has said to me “when looking for change don’t look at which position is best for change, but bring positive change in the position you’re in, that’ll take you to the positions that you can make bigger changes.” He is my hero, and so I laugh at this situation knowing he’ll overcome it. Good-luck to the people of Kano/ in Kano you’ll always be in my prayers and In Shaa Allah I’ll one day, like him, take a major part in helping you all with or without a political appointment. Thank you so much again! May Allah bless and guide us all 💙💙.

A post shared by Adam L Sanusi (@ashrafsanusi) on

 

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *