Rahotanni daga jam’iyyar APC na cewa, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar daya ne kadai bai yadda a fitar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ba tare da yin zaben fidda gwani ba.
Shugaban kwamitin da suke tantance ‘yan takarar, John Oyegun ne ya bayyana haka.
Ya bayyana hakane a jiya Juma’a ga manema labarai.
Yace duka sauran ‘yan takarar 22 sun amince a zabi mutum daya a bashi tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar ba tare da zaben fidda gwani ba.
Da yawa dai na tunanin Bola Ahmad Tinubu ne wanda bai yadda da zaben dan takarar na bai daya ba.