Inna lillahi Wa Inna Ilaihir Rajiun: Allah ya yiwa wanda zai yiwa Jam’iyyar PDP takarar majalisar Jiha a Ƙaramar hukumar Auyo ta jihar Jigawa, Hon. Adamu Musa (Sarki Ganuwar Kuka) rasuwa da daren yau sakamakon ciwon ciki, za’ayi Jana’izarsa da misalin ƙarfe 8 na safiyar yau.
Ko a jiya Litinin sai da Muryoyi ta ruwaito maku yadda wani dan takarar PRP shima yayi hadari ya mutu a hanyarsa ta komawa gida bayan yaje banki ya biya kudin fom din takararsa.
Daga Mansur Ahmed