fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Yanzu-Yanzu: Dan takarar Gwamna a Jihar Kano Malam Salihu Sagir Takai ya fice daga jam’iyyar PRP zuwa APC

Rahotanni da Hutudole ta samu shine, Dan takarar Gwamnan jihar Kano a shekarar 2019 Malam Salihu Sagir Takai ya bar jam’iyyar PRP inda ya kuma Jam’iyyar APC mai mulki a jihar Kano.

Mai magana da yawun Malam Salihu Sagir Takai Abdullahi Musa Huguma ne ya sanar da hakan ga manema labarai, inda ya bayyana cewa Takan da Magoya bayan sa sun fice daga Jam’iyyar PRP a ranar Litinin din data gabata.

Mista Huguma ya gaza bayyana dalilansu na barin jam’iyyar PRP da kuma zaban APC a matsayin jam’iyyar da suka yiwa komayya duba da tarun jam’iyyun siyasa da a ke dasu a Najeriya.

Karanta wannan  Mutane miliyan daya muka kashe domin a samu zaman lafiya a Najeriya, cewar shugaba Buhari

Sai dai ya ce an cimma matsaya ne bayan tattaunawa na dogon lokaci a tsakanin magoya bayan Takai.

Malam Salihu Sagir Takai dai, Haifaffan jihar Kano ne, kuma an haifeshi ne a shekarar 1960.

Takai ya taba rike Shugaban karamar hukumar Takai a shekara ta 1999 zuwa 2002 a jam’iyyar APP.

Haka zalika Takai Ya taba rike mukamin kwamishinan ruwa a zamanin mulkin gwamna Ibrahim Shekarau.

Ya kuma yi takarar Gwamnan kano a shekarar 2011, 2015, 2019, a jam’iyyun ANPP, PDP, PRP.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.