Dan takarar gwamnann jihar Borno a karkashin jam’iyyar PDP, Muhammad Jere ya bayyana cewa, sai ya kayar da gwamna me ci, Babagana Umara Zulum a zaben shekarar 2023.
Jere ya zargi gwamna Zulum da baiwa ‘yan uwa da abokansa kwangilar ayyuka a jihar Borno inda yace kuma ayyukan da ake yayata cewa gwamnan yayi basu da inganci.
Ya kuma kara da cewa, gwamna Zulum sai janye ‘yan jam’iyyar PDP yake zuwa APC a jihar, inda ya zargeshi da son mayar da jihar jam’iyya daya tilo.