Dan uwan shugaban Buhari, Fatuhu Muhammad ya fice daga jam’iyyar APC watanni uku bayan daya sha alwashin cewa sai ya rusa jam’iyyar.
Fatuhu ya kasance dan gidan Muhammad wanda shi kuma wa ne ga shugaban kasar Najeriya, wato Muhammadu Buhari.
Kuma ya fice ne bayan daya kasa samun tikitin komawa majalissa inda yake wakiltar Daura da Sandamu.
Yayin da shi a wannan zaben ma tun a na fidda gwani aka cire shi wanda hakan ke nuna cewa ba zai majalissa ba kuma ya matukar fusata.