fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Dan wasan Liverpool, Andrew Robertson ya ambaci sunan wani babban dan wasa da yafi Ronaldo da Messi

An tambayi Andrew Robertson shin tsakanin Ronaldo da Messi waye zakaran kwallon kafa na Duniya? Amma sai ya tsallake su yace kaftin din su na Liverpool, Jordan Henderson shine zakaran kwallon kafa na Duniya.

A Duniya gabadaya kowa yasan cewa Ronaldo da Messi sune zakarun kwallon kafa saboda nasarorin da suka samu a gasar kwallon kafa, Kuma sun kasance suna gasa tsakaninsu. Messi yaci kyautar Balloon d’Or har sau shida Ronaldo kuma sau biyar.
Masoya kallon kwallon kafa da yawa suna cewa Messi ne zakaran kwallon kafa wasu kuma suce Ronaldo ne. Amma ayayin da Andrews yake amsa tambayar da masoyan shi suka mai a shafin shi na yanar gizo yace kaftin din su ne zakaran kwallon kafa na duniya.
Liverpool na sa ran cewa zasu lashe gasar premier lig bayan an cire su a gasar champions league.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.