fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Dan wasan Manchester City De Bruyne yayi nasarar lashe kyautar Gwarzon dan wasan Premier League wannan kakar

Kungiyar Liverpool ne suka lashe kofin Premier League na wannan kakar, amma duk da haka dan wasan tsakiya na Manchester City De Bruyne ne yayi nasarar lashe kyautar gwazon dan wasan gasar Premier League a kakar 2019/2020. Tauraron dan wasan yayi nasarar kafa irin tarihin Thierry Henry na taimakawa wurin cinkwallaye 20 a kakar wasa guda kuma yaci kwallye 13.

Masoyan wasan kwallon kafa ne suka tabbarwa duniya cewa De Bruyne shine kwararren dan wasan wannan kakar na Premier League, kuma dan wasa yayi takara da yan wasan Liverpool guda uku wurin lashe wannan kyautar wato Trent Alexandra Arnold,Jordan Henderson sai Sadio Mane da kuma dan wasan Southtampton Danny Ings sai golan Brunley Nick Pope sannan dan wasan Leicester Jamie Verdy.
De Bruyne yana daya daga yan wasan da suka taimakawa Pep Guardiola a wannan kakar, kuma dan wasan yana cikin tawagar da Lyon suka cire jiya a wasan Quarter final na gasar Champions League da ci 3-1. De Bruyne ne yayi nasarar ciwa tawagar Pep kwallo guda amma wannan kwallon tashi bata hana Lyon cire su a gasar ba.
Dan wasan Belgium din ya kasance a kungiyar City har na tsawon shekaru biyar kuma ya buga masu wasanni 222 yayin da yaci kwallaye 57 kuma ya taimaka wurin kwallaye 89. Amma a wannan kakar wasasnni 48 ya buga kuma yaci keallaye 16 yayin daya taimaka wurin cin kwallaye 23.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Da Dumi Duminsa: Elon Musk zai saya kungiyar Manchester United

Leave a Reply

Your email address will not be published.