fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Dan wasan Manchester United Alex Telles ya kamu da cutar Covid-19

Alex Telles wanda koma kungiyar Manchester United a wannan watan daga Porto a farashin yuro miliyan 15.4 baya cikin tawagar Ole Gunnar Solskjaer da suka lallasa RB Leipzig 5-0 a gasar zakarun nahiyar turai daren jiya, yayin da kuma dan wasan mai shekaru 27 ya rasa wasan da Chelsea ta rike United 0-0 a gasar Premier League.

Alex telles ya zamo dan wasan United na biyu daya kamu da cutar bayan Pogba kamar yadda manajan kungiyar Ole ya sanar a jiya bayan sun kammala wasan su da Leipzig inda yake cewa, “Telles ya kamu da cutar korona saboda haka ne ya rasa wasu wasanni kuma babu alamun cutar a tattare da shi zai samu sauki bada dadewa ba”.
Manchester United bata yi nasarar cin wasa a gidan taba tunda aka fara buga wannan kakar amma jiya ta fara samun nasarara gidan nata cikin salo bayan tayi nasarar lallasa kungiyar Jamus Rb Leipzig 5-0 ta hannun Rashford wanda yaci kwallaye uku sai Greenwood da Martial suka ci sauran kwallayen.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  PDP yoyo take yi, ya kamata shugaban mu yayi murabus kan rikicin Atiku da Wike, cewar jigon jam'iyyar

Leave a Reply

Your email address will not be published.