fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Dangote ya karyata zargin da ake masa na goyan bayan wani Dan takara a Jihar Edo

Rukunin kamfanin Dangote ta karyata zargin da ke cewa Shugabanta, Aliko Dangote ya goyi bayan gwamna mai ci a jihar Edo, Mista Godwin Obaseki na sake tsayawa takara a karo na biyu.

Babban jami’in hulda da jama’a na rukunin kamfanonin Dangote Mista Anthony Chiejina ne ya musanta hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

Da yake mayar da martani ga wani rahoton da aka wallafa shi a yanar gizo wanda rahoton ya bayyana cewa, Dangote ya fada wa manema labarai a Abuja cewa “zai ci gaba da nuna goyon baya ga abokinsa na kwarai, gwamnan jihar Edo Mista Godwin Obaseki wanda ya shahara wajan nuna goyan baya ga rukunin kamfanin Dangote ta fuskar hada-hadar kasuwanci da kamfanin ke gudanarwa.

Karanta wannan  'Yan ta'adda sun kaiwa 'yan mahalissar jihar Baushi hari sun ji masu rauni tare da bata masu kadarori su yayin da suke gudanar da taro

A cewar Babban jami’in rukunin kamfanin Dangote Chiejina ya ce rahoton kawai soki burutsune da tsantsar karya.

Ya kara da cewa “Aliko Dangote dan kasuwa ne kuma jagorar kasuwanci wanda ya mai da hankali kan ci gaban kasa, samar da ayyukan yi da bayar da taimako. Chiejina ya kara da cewa: “Muna kira da jama’a da su yi watsi da duk wani batu na siyasa dake alakanta shugaban mu, ko kowanni rukunin kamfanin mu, muna tabbatar muku cewa Dangote baya goyan bayan ko wanne dan siyasa a jihar Edo dama sauran jahohin kasar nan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.