Attajirin dan kasuwarnan, Aliko Dangote ya sanya Najeriya ta shiga cikin kasashen da suke fitar da Siminti da yawa a Duniya.
Dangote ya fitar da Siminti zuwa kasashen Africa har tan 27,800. Hakan yasa ya zama na daya a Nahiyar Africa wajan fitar da Sumuntin.
Ana tsammanin nan da wasu makwanni Dangote zai kara yawan Simintin da yake fitarwa zuwa Kasashen Waje wanda hakan zai sa Najeriya ta kara samun ci gaba ta wannan fannin.

Kungiyar Masu Masana’antu ta Najeriya, MAN ta jinjinawa Dangote kan wannan nasara.
