Membobin jam’iyyar APC a jihar Nasarawa sun koma PDP bayan gwamnatin jihar taki cika masu alkauran kamfe da kuma magudin da sukayi a zaben fidda gwani.
Daruruwan matasa mata da maza ne suka taru suka babbaka tsinyoyi a jihar don a tabbatar da cewa sun sauya shekar.
Kuma jam’iyyar PDP ta karbe su da hannu biyu biyu bayan sun koma bayanta.