fbpx
Tuesday, May 17
Shadow

Dattawan Arewa sun soki Buhari kan rikicin Ganduje da Sarki Sanusi II

Kungiyar dattawan arewacin Najeriya ta yi watsi da ikirarin shugaban kasar da ke cewa ba shi da ikon shiga tsakani a rikicin masarautar Kano tsakanin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Sarki Muhammadu Sanusi II saboda tsarin mulkin Najeriya ya yi masa iyaka.

Kungiyar ta ce a matsayin shugaban kasar na jagoran al’umma, ba daidai ba ne ya tsame kansa ya koma gefe lokacin da wani abu da ka iya barazana ga zaman lafiya da tsaron wani sashen kasar ya kunno kai.
A cewarta yin hakan ba zai zama hawan kawara ga tsarin mulkin kasa ba.
Sai dai a martanin da ya mayar, shugaba Buhari ta hanyar mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu, ya ce shugaban a matsayinsa wanda aka zaba kan tafarkin dimokuradiyya ya san huruminsa.
“Idan lamari yana gaban kotu ko majalisa, shugaba Buhari ba shi da hurumin sa baki, domin idan ya sa baki ya karya doka.”


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

“Yana ganin gwamnatin Kano ita za ta magance duk wata matsala da ta taso da ke cikin huruminta,” in ji Garba Shehu.

Karanta wannan  Duk Ran Da Matasan Inyamurai Suka Dauki Ma*kami Ina Tabbatar Muku Najeriya Za Ta Zama Tarihi - Tsohon Sarkin Kano Muhammad Sanusi II

Amma dattawan na arewa na ganin akwai abubuwa da dama da shugaba zai yi ba sai kundin mulki ya ce ya yi wanda ba zai sa ya karya kundin tsarin mulkin ba.

A cewar Dr Hakeem Baba Ahmed, “bai dacewa a ce kana babba kuma ka ga ana rikici ka ki sa baki ba. Yana iya sa baki a rikicin Kano kuma akwai inda za a saurare shi a warware rikicin.”

“Amma kasa ido ka ce ba ruwanka, kuma kana matsayin shugaba akwai hakki,” in ji shi.

Ya kuma ce sun yi mamakin yadda shugaban ya nada wani kwamiti na daban duk cewa su suka fara zuwa Kano a matsayin dattawan arewa da nufin sasanta rikicin.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.