fbpx
Friday, February 26
Shadow

Dawowar Coronavirus/COVID-19:Gwamnatin tarayya tace akwai yiyuwar sake kulle makarantu

Kwamitin yaƙi da annobar korona na Najeriya ya ce wataƙila a sake rufe makarantu a faɗin ƙasar la’akari da ƙaruwar masu kamuwa da cutar.

A ranar Litinin aka sake buɗe makarantu a galibin sassan kasar, sai dai matakin ya janyo ce-ce-ku-ce.

Jami’an kwamitin da ministan ilimi da sakataren gwamnatin Tarayya na cewa wataƙila a sake nazari da rufe makarantu idan alkaluman masu kamuwa da korona ya ci gaba da ƙaruwa.

Jihohin Kaduna da Edo sun ƙi buɗe nasu makarantu saboda damuwar da ake nunawa na sake yaɗuwar cutar.

A wani labarin kuma gwamnati ta ce ta ba da kuɗaɗen da yawansu ya kai naira biliyan 10 domin samar da riga-kafin korona ƴar gida.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *