Sanatan jihar Kwara Ibrahim Oloriegbe ya bayyana cewa deliget din daya ba kudi a zaben fidda gwani sun dawo masa da abinsa daya fadi.
Ya bayyana hakan ne a ranar laraba inda yace ya basu kudin ne dama saboda wasu ‘yan dubaru, amma ya amshi abinsa.
Sanatan na daya daga cikin ‘yan majissar dattawan da suka bayyana cewa APC ta hana su tikitin komawa majalissar.
Kuma ya kalubalanci gwamnatin jihar Kwara cewa sun rigada sun fadawa deliget wanda zasu zaba.