‘Yan majalissar wakilai a jihar Bayelsa sunki tantance Ms Grace Ekiotene wacce aka zaba a matsayin kwamishinar kananun hukumomi.
‘Yan majalissar sun bayyana cewa ba zasu amince su tantanceta ba saboda batada kunya tasha saba masu a lokacin da take kwamishinar sufuri na jihar.
Ms Grace Ekiotene ta kasance tsohuwar kwamishinar sufuri a jihar kuma tasha samun sabani da ‘yan majalisar a lokuta da dama.
Saboda haka suma a jiya sun rama don sunki amincewa da ita, amma sun tantance sauran kwamishinonin da aka basu su tantance.
Hakan na nufin cewa yanzu Ms Grace Ekiotene tayi biyu babu domin tayi murabus ta nemi kujerar majalissa amma ta fadi zaben fidda gwani.