Wasu daga cikin yaran da hukumar ‘yan sanda ta ceto a ginin kasa na cocin jihar Ondo sunki amincewa su bi iyauensu su koma gida.
A karshen makon daya gabata ne hukumar ta ceto yara guda 23 da manya 55 a ginin kasa na wata cocin dake yammacin jihar Indo.
Kuma an kama faston da sauran manyan membobinta domin ana zargin cewa garkuwa sukayi da mutanen.
Yayin da su kuma yaran suka ce ba zasu taba bin iyayansu gida ba har sai an sako masu fastonsu da sauran membobin cocin da aka kama.