fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Direban motar daukar marasa lafiya ya yi wa mai cutar COVID-19 fyade a hanyar zuwa Asbiti

Lamarin ya farune a kasar Indiya bayan da a ka zargi wani Direban mator daukan mara lafiya Mai suna Noufal dan shekara 29 da laifin haikewa wata budurwa mai shekaru 19 wacce ke fama da cutar Coronavirus.

Direban wanda a ka tura shi domin ya kai mara lafiyan zuwa cibiyar killacewa dake
Pathanamthitta a daran ranar lahadi Wanda yayi dai-dai da 5 ga watan Satumba, amma gogan sai yayi amfani da damar hakan inda ya haikewa budurwar a kan hanyarsu ta zuwa Asbitin.

Da isar su Asbitin ne wannan budurwa ta shaidawa jami’an Asbitin abunda ya faru da ita.

Inda nan take jami’an Asbitin su ka sanar da Jami’an ‘yan sanda.

Daga bisani rundunar ta cafke Direban, haka zalika bayan bincike ‘yan sandan sun gano Direban bashi da shaidar karatu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.