
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Haka a kasar Japan, idan ka bari direban da ya sha giya ya bugu ya tukaka to kaima sai an kama ka da laifin barin mashayi ya jaka a mota.
A kasar Finland dole ka sayi lasisin jin waka a motarka, kamin ka samu saka kowace iein waka kake sonji.
Laifine da za’a iya kai mutum kotu akanshi, idan ka watsawa mutum ruwa lokacin da kake tukin mota a kasashen Ingila da Japan.
A birnin Manila, babban birnin kasar filifins an kayyadewa masu tukin mota ko sau nawa zasu tuka motocinsu a cikin sati, ana amfani da lambar motar mutum wajan kayyadewar.
A kasar Botswana sabawa dokane daukar dabba akan mashin idan dabbar zata karewa matukin mashin din gabanshi.
A kasar Sweden dolene mutum ya bar fitilar motarshi a kunne, hadda rana, idan aka kama mutum da fitilar mota a kashe to zaisha tara.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});