
Uwargidan Mataimakin Shugaban Kasa, Dolapo Osinbajo ta taya Uwargidan Shugaban Kasa, Aisha Buhari, murnar cika shekaru 50 a duniya.
Misis Osinbajo, a wani sako da ta wallafa a shafin Instagram a ranar Laraba, ta yi addu’ar ne ga matar Shugaban kasar, tare da yi mata fatan tsawon rai mai albarka.
