Tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi ya bayyana cewa, dolene a bar Inyamurai su karbi shugabancin Najeriya a 2023.
Yace ida akwai girmamawa da Adalci, Inyamuri ne ya kamata ya zama shugaban kasar Najeriya a 2023.
Ya bayyana hakane yayin da yake ganawa da wakilan PDP a ziyarar da ya kai jihar Ogun.
Tsohon gwamnan ya kuma yi kira ga wakilan jam’iyyar da cewa, kada su yadda da siyasar kudi a wajan zaben fidda gwanin dan takara na jam’iyyar.