fbpx
Sunday, February 28
Shadow

Dole Inyamuri ya gaji shugaba Buhari>>Kungiyar Kare muradin Inyamurai

Kungiyar kare muradin inyamurai ta jaddada matsayinta cewa shugaba dan kabilarsu ne zai gaji shugaban kasa, Muhammdu Buhari a shekarar 2023.

 

Kungiyar tace indai gaskiya da adalci za’a bi to Inyamurai ne zai mulki Najeriya a 2023, hakan zai kara kawo hadin kai a kasarnan, Inji Kungiyar.

 

Mataimakin me magana da yawun kungiyar,Mazi Chunks Ibegbu  ya bayyanawa manema labarai a Enugu cewa duk da ana tsaka da fama da Annobar cutar Coronavirus/COVID-19 kungiyarsu ba zata gaza wajan tallata manufofinta ba.

 

Yayi kira ga dukkan jam’iyyun siyasa a kasarnan da su tabbatar dan takarar kabilar Inyamurai suka tsayar inda da gaske ana maganar Najeriya 1 ce.

 

Da yake bayyana dalilin da yasa ya fadi waccan magana shine, a shekarar 1999, Obasanjo da Olu Falaye ne suka tsaya takara, a 2007 kuma marigayi ‘Yaradua ne da Muhammadu Buhari, a 2019 kuma Buhari da Atikune suka yi. Yace dan haka a 2023 duka inyamurai ya kamata a tsayar dan baiwa ‘yan Najeriya su zabi daya.

 

Kungiyar ta kuma taya sabon shugaban ma’aikatan shugaban kasa,Farfesa Ibrahim Gambari murnar mukamin da shugaban kasar ya bashi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *