fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Dole mu koyawa APC darasi kan zabar Musulmi da Musulmi data yi a matsayin ‘yan takararta na shugaban kasa, cewar wannan faston

Sam Ayedogbon, shugaban cocin Realm of Glory ya bayyana cewa dole au nunawa APC sakamakon babban kuskuren data yi na zabar Musulmi da Musulmi a matsayin ‘yan takararta na shugaban kasa.

Ya bayyana hakan ne biyo bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya zabi tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa.

Wanda hakan yasa fasto Sam yace jam’iyyar APC ta tafka babban kuskure kuma zasu yi amfani da katin zabensu son tabbatar mata da hakan.

Leave a Reply

Your email address will not be published.